Like On Facebook

Sabuwar manhajar AREWA24 na harin masu magana da harshen Hausa mazauna kasar waje fiye da mutum miliyan 8 kan farashin US$ 4.99 a kowanne wata.

Tashar Arewa24, tasha ta Hausa ta Arewacin Najriya ta na kaddamar da Arewa24 on Demand, wata sabuwar manhaja ta nuna shirye-shiryenta da ake kira subscription video-on-demand da “Over-the-Top” (OTT) a Turance.  Russell Southwood ya gana da shugaban Arewa24, Jacob Arback kan dalilan kaddamar da wannan manhaja da kuma abunda su ka shirya.

Tashar Arewa24 ta dade tana shirya kirkirar manhaja mai share fage kamar wannan.

Manufarmu ita ce hada kan masu magana da harshen Hausa da ke Arewacin Najeriya, da wadanda ke Najeriya baki daya, da kuma Hausawa mazauna kasashen waje a kan wata kafa domin kallon shirye-shiryen talabijin. Muna tsammanin samun muhimmiyar taskar adana shirye-shirye da suke da ingancin da ake bukata domin yin kafada-da-kafada da sauran shirye-shiryen kashashen duniya.

Arback ya kwatanta manhajar da manhajar “Netflix dan kallon shirye-shiyen Hausa”, wannan yana nufin manhajar ta kunshi shirye-shirye daban-daban wadanda su ka hada da wasannin kwaikwayo da kade-kade da motsa jiki da sauransu. Babu tallace-tallace a ciki haka zalika masu kallo zasu kalli duk abinda suke so kan kudi Dalar Amurka 4.99 tsawon wata guda da kuma kudi Dalar Amurka 48 tsawon shekara.

An kaddamar da manhajar ne a karshen watan Oktoba, za a iya sauke manhajar daga shafin Arewa24 inda za ku samu manhajar da zata dace da wayoyinku masu amfani da tsarin iOS da kuma na Android. Kafar Google Play ta bayyana cewa kawo yanzu, fiye da mutum 500,000 suka sauke manhajar. Haka kuma za a iya samun manhajar a kan kafafen Roku da Amazon Prime haka kuma nan gaba kadan za a iya samun manhajar a kan wasu kafofin.

“Yadda muka tsara shi ne, mukan dora shirye-shirye kyauta kan shafin YouTube tare da sako mai zayyanawa masu kallo cewa zasu koma kallo a kan wannan sabuwar manhajar daga 21 ga watan Nuwamba. Muna so mu fara da masu kallonmu da ke kasashen Saudi Arabia da Sudan da Amurka da kuma na nahiyar Turai” Shugaban ya nuna cewa wannan tsarin ya fi sauki ga masu magana da harshen Hausa da ke ko ina a duniya fiye da tsarin tauraron dan dan’adam.

Arewa24 tana aiki tare da masu shirya fina-finai masu zaman kansu na Arewacin Najeriya wadanda Arback ya kira da ”Hazikan marubuta da suka kware wajen iya bada labari, Arback din ya kara da cewa, babu abun da suke bukata sai jari dan su habbaka su zamo kamar masana’antar Nollywood dake Kudancin Kasar. Muna aiki tare da wasu masu shirya fina-finai wadanda suke shirya fina-finai na musamman.”

Shirye-shiryen da aka fi maida hankali akai su ne rubutattun wasannin kwaikwaiyo da tashar ta shirya. Wasannin sun hada da shararrun wasannin kwaikwayonmu masu dogon zango wato “Kwana 90” da kuma “Dadin Kowa” wanda shi ne shirin wasan kwaikwayo na farko da tasha mai zaman kanta ta shirya. “Za mu samar da wani shirin wasan kwaikwayo a shekara mai zuwa. Masu Magana da harshen Hausa su na son wasannin kwaikwayo. Wasanni ne masu nuni da al’adu da rayuwar yau da kullum amma cikin kyakyyawan tsari.”

Dadin dadawa, sabuwar manhajar za ta kunshi dukkannin shirye-shirye da ke kan tashar wadanda suka hada da shirye-shiryen Hip Hop da na girke-girke da shirye-shiryen yara da na motsa jiki (wanda ya kunshi sharhin Gasar Premier League ta Nahiyayar Turai da manya-manyan gasar kwallon kafa da ake gudanarwa a birnin London wadanda aka juya zuwa harshen Hausa). Haka kuma akwai bangaren takaitattun shirye-shirye wadanda suka kunshi shirye-shiryen yara da wasannin barkwanci da kananun shirye-shirye da kuma gajerun fina-finai. ”Muna da wani shiri da mai’akatanmu na shashen sada zumunta suka tsara wanda suke fita su na tambayar mutane tambayoyi ma su ban dariya.”

Yaya matsalar yanar gizo da ake fuskanta za ta yi tasiri ga wannan manhajar? “Da farko dai manufar wannan manhajar ita ce nishadantar da masu magana da harshen Hausa mazauna kasashen waje. Tasharmu tasha ce da take kai wa kai tsaye ga wasu kebantattun mutane mazauna kasashen waje: Hasashe ya nuna cewa da akwai Hausawa mazauna kasashen waje kimanin miliyan 8 zuwa 10 wadanda ke zama a Saudi Arabia da kuma Sudan. Mazauna Arewacin Najeriya za su iya sauke manhajar kuma za ta zo musu da wani yanayi wanda zai daidaita matsalar yanar gizo da ake fuskanta.”

Ma su kallo mutum nawa ya ke hasashen samu nan da shekara 2-3?. “Ba na ce ba. Yanzu haka muna da masu kallon shirye-shiryenmu a shafin YouTube mutum miliyan 50 amma mun zuba hannun jari kuma muna da kyakkyawan zato game da manhajar.  Za mu rika kawo sababbin shirye-shirye a kullum kuma a kowanne mako. Mu na san mu samar da shiri 11-12 a kowacce rana, dan haka zai yi kyau a samar da wata kafar yada shirye-shirye dan wasu ma su samu damar kallo.”

Wanne irin matakin hannun jari aka zuba cikin wannan manhajar? “Duba ga yanayin tasharmu dai babban hannun jari ne, amma ga matakin duniya an yi abu na azo a gani. Muna so mu zama mu ne na farko wajen kirkirar irin wannan manhajar. Tara shirye-shiryen shi ne abu na farko. Yanzu muna da kimanin sa’o’i Dubu 45. Rabin wadannan shirye-shiryen kadai na aka samu damar dorawa a kan manhajar kasancewar sauran aikin da ya rage ya yi nauyi saboda ingancinsa.”

The post Sabuwar manhajar AREWA24 na harin masu magana da harshen Hausa mazauna kasar waje fiye da mutum miliyan 8 kan farashin US$ 4.99 a kowanne wata. appeared first on AREWA24.source https://arewa24.com/manhajar-arewa24-on-demand-na-harin-mutum-miliyan-8/
Advertisements

Post a Comment

0 Comments